Makaranta Mallam
Bambadiya

Shekara 10 ke nan da muka assasa wannan MAKARANTA a sahar Fesbuk, kuma cikin tsawon rayuwar da ta yi, an samu nasara ƙwarai da gaske.

Kamar yadda muka ambata a lokacin kafa MAKARANTAR, mun yi ishara da cewa za a sake wa makarantar fasali da tsari don ta dace da zamani. To da alama lokaci ya yi, bayan suma na kusan shekaru. Allah ya taimaka, ya kuma ci gaba da yin jagoranci!

Ba sai an nanata ba, rubutu kowane iri yana da rawar da zai iya takawa wajen ciyar da al’umma gaba. Saboda haka SABUWAR MAKARANTAR MALAM BAMBADIYA  za ta ci gaba da gudanuwa ne saboda a ga yadda za a iya gyara ko inganta rawar da ake yi yanzu a fagen ci gaban adabin Hausa da kuma irin kiɗin da ke tashe da yadda za a aza sabo don taka rawa mai birgewa. Fatarmu ita ce za mu yi ƙoƙarin aza darussan da za su taimaka wajen inganta rubutun Hausa kowane iri ne (zube da waƙa da wasan kwaikwayo) bisa turbar da zamani ya tanada ta yadda adabin Hausawa shi ma zai shiga cikin tsara da sanya tufafin gani da faɗa.

Darussan da za mu mayar da hankali kai a wannan sabuwar MAKARANTA, su ne:

  1. Waiwayen baya don gyaran yanzu da kuma gaba a harkar adabin Hausa.
  2. Me ya sa ake rubutu da irin ribar da za a tsinta wajen yin sa?
  3. Yaya ake rubutu kowane iri, domin ya dace da zamani?
  4. Hanyoyi da za a iya bi domin inganta rubutu kowane iri cikin Hausa.
  5. Yaya za a kitsa saƙon rubutu don ya dace ga makaranta da sauran al’umma?
  6. Yaya salon rubutu mai kyau da burgewa yake?
  7. Yaya za a gina zubi da tsarin rubutu mai armashi cikin Hausa.
  8. Waɗanne hanyoyin za a bi domin samar da ire-iren hanyoyin tsara da buga littattafai a ƙasar Hausa da ƙasashen waje.
  9. Hanyoyin kasuwancin littattafai domin isa ga yawancin al’umma da kuma samun riba.
  10. Matsayin marubuta da hukumomi daban-daban (Gwamnati, WAEC, NECO, IJMB, JAMB, NERDC, MAKARANTU DA JAMI’O’I).
  11. Za a dinga gabatar da ayyukan yi a gida da jarabawa da fitar da sakamako da ba da satifiket.

A lokacin da ake gudanar da wannan karatu, SABUWAR MAKARANTAR MALAM BAMBADIYA ta tanadi hanyoyin da za a bi a ga an ci moriyar wannan karatu ba kurum a cikin makarantar ba, har lokacin da aka sauke karatu, aka shiga duniyar yau da kullum.

Daga abubuwan da aka tanada ko ake niyyar tanada da akwai:

  • Daga lokaci zuwa lokaci SABUWAR MAKARANTAR MALAM BAMBADIYA za ta shirya tarurrukan ƙara wa juna ilmi a wata jami’a ko tsangayar ilmi domin marubuta da masana da manazarta su yi kwamba don samun ƙarin ƙwarewa da gwanancewa a fagen rubutu.
  • SABUWAR MaKARANTAR MALAM BAMBADIYA za ta dinga shirya gasa ta musamman domin fito da zaƙaƙuran marubuta waɗanda za su kasance fitilun gobe a fagen raya adabin Hausa.
  • SABUWAR MAKARANTAR MALAM BAMBADIYA za ta kuma keɓe MAKO NA MUSAMMAN domin tunawa da marubuta ‘yan mazan jiya da irin gudunmuwar da suka bayar a fagen raya adabin Hausa.
  • Za a kuma dinga shirya MAKO NA MUSAMMAN domin yaba wa zaɓaɓɓun gwarzayen da suke taimakawa wajen ci gaban adabin Hausa ta hanyar ba su GARKUWA.
  • Za a kuma kafa wata Tsangaya da za ta mayar da hankali wajen fassara fitattun ayyukan adabin da SABUWAR MAKARANTAR ta samar zuwa harsunan Ingilishi da Larabci da sauran fitattun harsuna don a san da zaman marubutan Hausa a duniya.
  • Makarantar za ta kuma taimaka wajen tace da tsara da buga waɗansu ayyukan da ta ga sun cancanci a buga, musamman idan marubutan ayyukan ba su da ƙarfin buga ayyukan nasu.
  • Haka kuma za a samar da ɗakin karatu na musamman da marubuta za su iya leƙawa domin nazari da ƙarin ilmi a cikin Kibɗau ɗin.
  • MAKARANTAR za ta kuma mayar da hankali wajen sanya shauƙin rubutu ga ‘yan makarantar Firamare da Sakandare ta hanyar shirya gasa tsakanin makarantun da kai ziyara da fito da tsarin GA-NI-GA-KA/KI tsakanin makaranta da marubuta.
  • SABUWAR MAKARANTAR za ta zama tamkar jakadiya tsakanin marubuta da Gwamnotoci da Hukumomi da ɗaiɗaikun mutane da suke sha’awar ci gaban adabin Hausa ta hanyar samar da ɗauki ga marubuta duk lokacin da hakan ya taso.
  • SABUWAR MAKARANTAR za ta sake dubar yiwuwar ƙulla dangantaka ta musamman da kafafen watsa labarai domin ci gaba da yayata ayyukan marubuta da adabin Hausa.
  • Haka kuma SABUWAR MAKARANTAR za ta samar da matsuguni na musamman (kyauta) da marubuta za su zauna a ciki na tsawon wata ɗaya zuwa biyu, suna nazari da rubuce-rubuce cikin tsanaki, ba tare da hayaniyar duniya ba.

DAIDAITACCIYAR HAUSA DA ƘA’IDOJINTA JIYA DA YAU!

Tarihin rubutu da karatu irin na boko a ƙasar Hausa da muka sani ya biyo matakai-matakai a tsawon tarihi, wanda daga nan ne aka samar da ƙa’idojin rubutun da kuma samar da Daidaitacciyar Hausa. Tun daga farko dai abin da ya dace mu fahimta shi ne tun kafin zuwan Turawa

Read More »