Fassarar labarin Sada Malumfashi daga harshen Ingilishi zuwa Hausa daga Saifullah Ibrahim Gusau.
- Ta yi rawa a tsirara.
- A wannan daren da Inna ta yi rawa tsirara a bakin masallaci, iyakacina shekara bakwai. Ruwan sama ne ke sauka da ƙarfi a yayin da Inna ta zo tana kaurar ƙofa tana ƙwala wa Mama kira. Ɗoyin jikinta ya surnano ta huɗuwar makullin ƙofa, ya bugi hantunanmu ya fizgo mu daga bacci. Wuraren ƙarfe huɗu ne, kusan lokacin sallar asubahi. Ta ture ƙyauren gida, ta antaya cikin ruwan saman ba tare da tufafi ba. Ta yi ta tiƙar rawa a bakin ƙofar masallaci yayin da bayin Allah ke rusunawa suna bautar Ubangiji, a daidai lokacin da muryar Ladan da ta Inna ke faman shillo a cikin iska.
Da masallatan suka sallame sallar sai suka same ta tsirara ruwa na dukan fatar jikinta, yayin da take buga ƙafafunta a ƙasa tana fantsalar da ruwa. Da safe muka tarar da ita tana kyarma a ɗakinta. Kawu Umar ne ya same ta tare da wasu daga cikin masallatan bayan sallame salla. Kasancewar ya san shaƙiyyacinta, wannan ya sa ya farmake ta da bulalar doki, ya zane jiƙaƙƙen jikinta har sai da ta dawo garau. Raɗaɗi ya yi aikin korar iskokai.
Inna ta kasance tana ziyartar gidanmu. Na shafe wani kaso mai yawa na ƙurciyata wurin kallon tafiyarta da zuwanta. Mafi yawan lokuta da daddare take tafiya, a tsumma, a gajiye, da ‘ƴan komatsanta a yakutacciyar jaka mai ƙunshe da ‘ƴan kaya da tulin magungunan asma. Hucin da take ne ke alamta isowar ta daga nesa.
Matan dangimu kan tsegunta labarai a kan Inna a bukukuwan suna ko aure. Wai ta haukace ne saboda mijinta ya auro wata matar. Tun lokacin ta fara yawo daga wurin wannan ɗan’uwa zuwa wannan, gari ya gari, takan yi tafiyar ɗaruruwan kilomitoci a ƙafa. Idan ta iso mafi yawancin lokuta nakan dibi bororon da ke ƙafafuwanta, da kumburarrun cinyoyinta da baƙin cikin da ke fuskarta, wanda ke labarta nisan tafiyar da ta ciwo. Baba shi ne ɗan gaban goshinta a cikin danginmu, shi ne bai taɓa ɗaga hannu da niyyar dukan ta ba, ko ya zane ta idan ta yi fitsari a cikin kwanon abincinta ba. Yakan jure halayenta sosai har ta kai takan jima idan ta zo gidanmu kuma ta fi ziyartar mu bisa ga kowa.
An keɓe mata ɗakin da take zama idan ta sauka. Ranakun farko na isowarta ne kawai ake samun damar mu’amalar hankali da ita ba tare da wani jidali ba. A ganina tana da kunya, ba ta faye magana ba, kuma kowa takan kira shi da sunansa. A ranaku biyun farko za ka same ta lafiyayyar talika, tana cin abinci da kyau, tana kashi a ban-ɗaki, tana kakkafta ɗakinta. Sai fa a rana ta uku ne ɗakin ke fara tsami, za a isko ta shasshafe zannuwanta da kashi, kwanoni da kofuka kuwa cike da fitsari. Daga nan sai sauran ranakun su zama abin ban tsoro ga dukan mutanen gidan.
Ba zan iya bambance shin masifarta da kuwwace-kuwwacenta a tsakiyar dare ƙirƙirar mafarkaina ne ba ko kuwa koke-koken ne ke ingiza ni yin mafarke-mafarken. Sunan Mama kodayaushe shi ne a bakinta idan abin ya motsa. Baba bai fiye zama gari ba mafi yawancin lokuta sai a ‘yan kwanaki bayan kowanne makwanni biyu; saboda yana tafiya wurin aiki. Kuwwace-kuwwacen kan soma ne da saukar duhu, wani irin ƙugi mai tashi da taratsi da ke gasa da na tsanyoyi. Mafi yawan lokuta tsinar mijinta take yi, ta yi ruwan zagi da tsinuwa a kan matarsa, can kuma sai ta fara magiya wai a zo a cece ta, ko ta ce asmar ta taso ta dinga kukan ƙarya. Idan Inna ta fara maimaita sambatunta sai na dafe kunnuwana da hannuwana, na kwanta a duƙunƙune kamar kwanciyar ɗan tayi, ina yi wa kaina umurnin farkawa daga mummunan mafarkina ko kuma na yi fatar komawa bacci. Da ƙyar nake iya bacci a waɗannan ranakun kuma rayuwar zahiri kan zame mini wani irin dusashen hoto.
Da rana na bi ta ƙofar ɗakinta da hannuwana kunkume da ƙarfi a bisan hancina don na ƙetare mugun ɗoyin ɗakin. Da daddare mu rakuɓa jikin juna, mu duka ni da Mama da ƙanwata a kan gado ɗaya muna masu ƙoƙarin nutsar da ƙarar fuskarta cikin duhu.
Shekarata goma lokacin da ƙanwata mai shekara takwas ta fara furuci da harshen da na kasa fahimta. San da abin ya fara, idanunta suka koma jaja-jaja, halayyarta ta lalama ta koma ta masifa. A irin waɗannan lokuta, sai Baba da Mama su ɓoye ta daga gare mu tana fizge-fizge tana ture su daga gare ta wani lokaci har ta tunkuɗe Mama ta faɗi ƙasa. Sai Zulai ta saki wata irin kururuwa sannan ta yi gurnani da dariya. Hawaye kan gangaro daga idanunta, amma bakinta a buɗe yana kwarara dariya. Sai a sanya kaset mai naɗin karatun Ƙur’ani a na’urar rakoda, karatu ya yi ta gudana ba tsayawa yayin da aka banƙare ta ana tursasa ta saurare don a samu aljanun su fita. Sai na sulale na ɓoye a ɗakina, na koɗe zuciyata yayin da sautin karatun da kururuwar zulai ke tashi suna tokare silin.
Masu magani mabambanta suka ci gaba da zirya a gidanmu don su yi mata addu’a. Sukan tofa yawu bisa kanta su karanta ayoyin Alkur’ani su roƙi aljanun su fita kafin a sakar musu ruwan bala’i.
Ba dai wani ci gaba da aka samu, don haka Mama ta faɗaɗa harkar ta hanyar ziyarar wasu masu maganin. Daga ta zo da ƙulle-ƙullen ganyayyakin da za a barbaɗa a cikin nono; sai kwalaben haɗe-haɗen magungunan gargajiya da za a tsosa, sai turaren wuta da akan barbaɗa cikin garwashi wanda hayaƙinsa za a sa Zulai ta shaƙa sai ta kusa suƙewa, sai kuma magungunan da za a barbaɗa a ruwan wanka, safe da yamma. Amma ciwon ya ci gaba kamar abin da ake ƙara zugawa. karatun Alkur’ani ma ya ci gaba, ta nan ɗin ma ba wani sauyi..
Mai magani na gaba da ya zo, wani sangami da shi mai dogon gemu. Yana da ɓula-ɓulan idanu jajaye, kamar wanda ya taso daga bacci mai nauyi. Akan gayyato masu maganin ne idan ciwon ya motsa ko bayan lafawarsa. Amma wannan ɗin a san da ya zo rashin lafiyar ba ta tashi ba. Na ɓoye bayan kujera don na ji abin da ke wakana sannan in ƙirƙira hotunan daga zancen, na kunna su cikin kwanyata. Ya fara ne da karanto wasu addu’o’i da Larabci kafin ya fara tattaunawa da ita da Hausa:
“Mene ne sunanki?”
“Zulai”
“Ya jikin naki?”
“Lafiya lau”
“Ina so yanzu ki natsu ki saki tunaninki. Ki bar komai ya zo.”
Ya ci gaba da ruƙiyyarsa sai ga kururuwar nan tata sananna ta ɓullo. Da ya dawo da ciwonta, zuciyata ta tarwatse, ɓalli-ɓalli. Me zai sa mai magani ya tada ciwon da ya lafa. Can muryarta ta sauya. Yanzu matar da ke magana ba ƴar’uwata ba ce. Wata babbar mace ce, tana nishi sama-sama tana faɗin a yi mata rai.
“Na rantse zan fita,” sabuwar muryar ta yiwo ihu, amma mai maganin ya ci gaba da ruƙiyyar bai dakata ba.
“Na rantse ba zan komo ba,” muryar ta ƙara kuwwatawa a sauti mai ban tsoro.
Can sai ruƙiyyar ta tsaya. Sai na ji duk na ruɗa kaina da tambayoyi: to ina Zulai, kuma wace ce tare da su a ɗakin? Na yi ƙoƙarin farkar da kaina daga wannan mafarkin amma na kasa, yayin da dandazon muryoyi ke yin gumurzu a cikin kaina. Zantuttuka suka yi ta dawo mini, tunane-tunanena suka ɓata daga kaina. Na fito na tarar Zulai har ta yi bacci a hannun Baba, a kan gado. Daga ranar Zulai ta wartsake ba tare da tashin wani abu ba, ta bar ni da kaɗaincin nemo ɗan zirin da ya bambanta zahiri da kuma yaye-yayen mafarki.
A ranar da na cika shekara sha-biyar ne na fara jin abubuwa na saukar mini kamar saukar jifa. Ɓacin rai, na ji kaina ga ni nan dai, cikin wasu yanaye-yanaye masu kama da yanke ƙauna da rashin jin ƙimar kai, kuma ma har ba na jin daɗin abubuwan da nake so sosai. Jikina ya rataye a wani sarari tsawon ranaku. Waɗannan ranakun suka maido mini da walƙiyar tunane-tunanen Inna. Na ƙoƙarta amma na kasa gano yadda ta iya jure rayuwar tafiya koyaushe da kuwwar dare. Mene ne yake wasa da hankalinta, yake cin jikinta, yake sanya ta yawo kullum, gaba da baya?
Na san abin da ke damu na wani irin ciwon ƙwaƙwalwa ne kuma ina burin fizgewa daga gare shi in yi ta kuwwa cikin dare. Na yi nazari a intanet da kuma ‘ƴan littattafan da ke cikin maktaba yayin da nake shirya wa karatun makarantar koyon likitanci. Amma ba na so in yarda cewa abin da na gano shi yake damu na. Don haka sai na yi wuridin sunayen alamomin: Ciwon Damuwa, Cutar fargaba, Taɓin Hankali, Dimenshiya, Cutar kaɗuwa, Hauka. Daga ƙarshe kuma sai na yi watsi da su saboda alamun cututtukan na da ban tsoro. Ba na so na yarda da cewa ina ɗauke da alamun da ake buƙata wurin tabbatar da aukuwar ɗayan cututtukan.
Ni mai yawan addu’a ne, don haka ba zai yiwu in faɗa cikin komar wani aljani ko bakin mutane ba. Ni da ke yawan yin addu’a: nakan ɗauraye jikina daga dukan sharri ta hanyar alwala sau biyar a rana, wata rana har da daɗin wata alwalar kafin in kwanta bacci. Addu’ar safe daban ta dare ma daban, kuma nakan tofe kafaɗuna da addu’ar don korar dukkan sharri, ayoyin Alkur’ani su ne abokaina da safe kuma su ne abokaina da dare. Don haka ciwona wani abu ne daban, na tabbata ba damuwa ba ce, gajiya ce kurum. Alamun kan zo su koma. Ba wani abin tayar da hankali ba ne.
Amma kuma sai in ji ina kwaɗayin kaɗaici. Har ma nakan rufe kaina a ɗaki tsawon ranaku. Ranakun da Mama ke kira ranakun kaɗaicina, kuma takan ce wai zan koma daidai na karkaɗe. Gudummawarta a wurin magance wannan matsalar ita ce ƙona turaren wuta da ganyayyaki, wanda hayaƙinsu kan shiga tsakanin hannuwan fanka masu wulwulawa a cikin ɗakina.
- Ina da shekara goma sha bakwai a lokacin da wani gagarumin al’amari ya faru. Ga yadda nake iya tuna al’amarin: a dare wata rana na tashi da misalin ƙarfe uku, ina tattakawa a cikn duhu ina tangaɗi. Sai na ji kamar kaina ya zama ƙafafuna, saboda in gane ko a birkice ne nake tafiya sai na kunna fitila na dubi madubi, ai kuwa sai gani na yi kamar madubin na yi mini ƙarya, don kuwa nuna mini ya yi wai a miƙe nake daidai, amma kuma ni ina jin lallai a jirkice nake don kuwa na ji kamar jini na sauka cikin kwanyata. Nan take na naushi madubin, nan da nan surata ta zama fasassa a jikin madubi. Baba ya rugo cikin falo, ya kama ni ya rungume ni yayin da nake ƙoƙarin daidaita tsayuwata, ina tsoron jirkitar da shi shi ma. Ya tanƙware ni, na narke a ɗumin jikinsa yayin da muka tashi sama tare, a sararin iska, muka yi bacci a rataye.
Ga yadda aka ce mini abin ya faru: na tsuguna ne kusa da shimfiɗar ƙanena ɗan shekara biyu. Abba yana kuka cikin dare na cira shi sama, na rarrashe shi ya yi bacci, sai na fara buga kansa a ƙasa cikin wani irin salo. Na ƙyalƙyace da dariya. Baba ya shigo ya kame mini kunkuru ya riƙe ni. Mama ta faɗi ƙasa. Ɗanta na kwance a ruwan jini, farin zanen shimfiɗarsa duk ya yi jagab da ja. Baba ya fitar da ni daga ɗakin, hannunsa zagaye da jikina mai makyarkyata. Numfashina na fita a hankali, amma dariyata ta ƙi ta dakata.
Da safe Baba ya gina rami mai zurfin ƙafa biyu, ya binne Abba. Aka ce wa mutane ya mutu ne sanadiyyar matsanancin zazzaɓi da daddare. Watannin da suka biyo na yi ta buga kaina a kan daɓe daidai wurin da na fasa kan Abba, jini ya ɓulɓulo ya kwanta. Daga nan kuma na zama fursuna a ɗakin Inna. A waɗannan lokutan kaɗainci na yi mararin zuwan Inna ko don ta faɗa mini yadda take samun natsuwa daga tafiye-tafiye masu nisa da take yi da kumburarrun ƙafafu.
Mama kan yi zaman tamataila a ƙasa daga gefen ɗakin tana kallo na, ta yi tagumi, abincin da ta sa gaba kan yi sanyi, ƙuda na bibiyar sa.
“Yi haƙuri Mama,” na ce mata, daga turke a kan gado. Ta tashi, tana tangaɗi, kwanon abincin ya kife a ƙasa, ta ruga zuwa ɗakinta.
Ba zan iya tuno abubuwa da yawa daga wannan lokacin ba, amma zan iya tuna ɗanɗanon ɓacin rai. Da yadda Mama kan zauna cin abinci tana gunguni tana ƙoƙarin kinnewa, tana daddanna adiko a kan idanunta har suka yi ja, hawayen suka ƙafe. Zan iya tuna shiru da sirrika da labaran da ba su taɓa wuce katangar gidanmu ba. Da yadda na yi mararin jin koke-koke da kuwwace-kuwwacen Inna, ko na samu na toshe kunnuwana da yatsuna don na farka daga wannan azababben mafarkin.
6
Muna tsakiyar wani kwas na makarantar koyon likitanci ne wayata ta buga.
“Alo. Baban Zulai ne?”
“Alo. Wanta ne. Me ya faru?”
“Dan Allah ana buƙatar ka zo hostel ɗinsu yanzu-yanzu “
Layin ya tsinke. Na damƙi “stethoscope” ɗina na nufaci wurin ƙanwata mai shekara ashirin. Na same ta a asibitin makarantar, nas uku sun daddanne ta. Ta watsar da su ƙasa kamar sarauniyar yaƙi. Kayanta sun yi burum-burum da ƙura, gashinta kuma ya tsikare sama yayin da take gurnani tana ƙoƙarin kubcewa da ƙarfin tsiya. Wata nas ta sunkuya kanta tana karanta mata ayoyin linjila, amma kamar ƙara fusata Zulai wannan yake yi kurum. Muka haɗa ido. Ta gane ni, sai ta kubce daga gare su ta faɗa a cikin hannuwana. Na rarrashe ta, hawaye na taruwa a idona. Na ji ilahirin jikinta na rawa a manne da nawa. Ta ce na gaya musu su daina yi mata dariya. Na yi mata alƙawari za mu kama su mu hukunta su. Sai ta natsu.
Wannan shi ne karon farko da ciwon Zulai ya tashi tun zuwan wannan mai maganin shekaru da dama da suka wuce. Kodayake wannan ya sha bambam. Tana gani kuma ta ji abubuwan da ba na iya gani a cikin yanayin ɓatan- kai da ɓatan-basira kamar yadda zan iya tunawa daga darasin lafiyar ƙwaƙwalwa. Wani abu ya ci gaba da damun ta duk da alƙawarin da na yi na kare ‘ƴar ƙanwata, ba abin da na iya yi. Ciwon ya ci gaba da tashi lokacin da ya ga dama, tofe-tofe da ganyayyaki da hayaƙin da Mama ke yi bai taɓuka komai ba. Daga nan kuma ba ta sake warkewa ba.
7
Wata rana ina zaune a ƙarƙashin icen gwaba inda labaran rayuwar ƙurciyata suke a jibge, guntu-guntu. A wurin da aka binne fasasshen ƙoƙon kan Abba tare da wani guntun sashen rayuwata a shekarun da suka shuɗe. Zulai ta kwanta a rigingine a ƙasa, kanta a kan cinyata tana ƙidaya ɓoyayyun magautanta maras adadi da za su kawo mata farmaƙi su sarƙe gashinta da zaran na tafi bikin rantsar da ni aikin likitanci gobe. Na ɗau dutse na ƙyare kan wani da ya laɓe bayan ice. Ta yi ruri ta shiga faɗan. Muka cigaba da jifar ganyayyaki da tsuntsayen da ke waɗari a cikin masifaffen hadari. Na sumbaci Zulai a kan kunci, na jawo ta daga abokan faɗanmu da muka rinjaya zuwa cikin gida. Amma sai ta tuɓe kayanta, ta yi tsalle ta faɗa cikin taɓo, ruwa na sauka suna wanke dattin gashinta. Na so in jawo ta mu ruga cikin gida amma sai na tsaya, ni ma na tuɓe kayana, muka yi ta rawa a tsirara, wannan ya zama tamkar aikata wata ibada ce da ka iya maido mana da tunane -tunanenmu da suka sarƙe.